Home Labaru Kwazo: Cristiano Ronaldo Ya Ci Newcastle Kwallo Biyu A Wasan Farko A...

Kwazo: Cristiano Ronaldo Ya Ci Newcastle Kwallo Biyu A Wasan Farko A United

11
0
Ronaldo Manchester

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo biyu a wasan farko da ya buga wa Manchester United a karawar da ta doke Newcastle United ranar Asabar.

United ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan mako na hudu a Premier League, inda United ta yi nasara da ci 4-1 a Old Trafford.

Ronaldo wanda karo na biyu da ya koma United a bana daga Juventus ya fara cin kwallo daf da za su je hutu, kuma na farko da ya ci a raga tun bayan shekara 12 da kwana 124.

Rabonda kyaftin din tawagar Portugal ya ci wa United kwallo tun cikin watan Mayun 2009 a wasa da Manchester City.