Home Labaru Matakan Hukumomin Tsaro: Barayin Daji A Najeriya Sun Shiga Rudani

Matakan Hukumomin Tsaro: Barayin Daji A Najeriya Sun Shiga Rudani

25
0
Nigerian Army

Matakan da ake dauka don dakile ayyukan barayin daji a Najeriya sun fara tasiri a kan ‘yan bindigan , wadanda yanzu haka rahotanni ke nuni da cewa sun shiga rudani, sakamakon rashin man fetur da sauran mahimman abubuwan bukatar su.

A makon da ya gabata ne jihohin da wannan  al’amari na barayin daji ya  fi shafa kamar su Zamfara, da Katsina, Neja da Kaduna suka ayyana dokar haramcin sayar da man fetur a jarka da kuma cinikin shanu, har da rufe kasuwannin mako-mako a wasu wuraren da zummar taka wa barayin birki.

Kari a kan wadannan matakai shine rufe hanyoyin sadarwa a Zamfara, biyo bayan bukatar da gwamnatin jihar ta mika.

Rahotanni da ke fitowa daga arewa maso yammacin Najeriyar na nuni da cewa ‘yan bindigan sun shiga mawuyacin hali na yunwa da rashin mahimman abubuwan bukata, har ma yanzu su na karbar shinkafa da taliya a matsayin abin fansa.