Home Labaru Zaben 2023: Kudu Ta Manta Da Kujerar Shugaban Kasa -Junaid Mohammed

Zaben 2023: Kudu Ta Manta Da Kujerar Shugaban Kasa -Junaid Mohammed

667
0

Tsohon dan majalisar wakilai a jamhuriya ta biyu, Junaid Mohammed, ya ce kudancin Najeria su manta da samun kujerar shugaban kasa a shekarar 2023 matukar arewa za ta tsayar da dan takara.
Tsohon dan majalisar ya yi ikirarin cewar tsarin mulkin karba-karba a tsakanin yankunan Najeriya ya lalace, saboda haka duk yankin da yake da yawan jama’a shi ne zai samar da shugaban kasa, ya zargi ‘yan kabilar Igbo da karbar miliyoyi domin goyon bayan Atiku Ababukar a zaben da ya gabata.
Junaid, ya ce an hada baki da mutanen da ya kamata su kare doka wajen tafka murde zaben shekarar 2019, amma kwata-kwata baya son jin tsarin karba-karba saboda maganar kawai ce.
Junaid Mohammed, ya kara da cewar mutanen kudu, musamman na yankin ‘yan kabilar Igbo, ne suka fara lalata tsarin karba-karba ta hanyar kin bayar da kuri’unsu ga duk dan takarar da aka tsayar domin tabbatar da tsarin.
Ya kara da cewa jama’ar yankin kudu maso gabas, na ‘yan kabilar Igbo, sun ki koyar darasi daga irin kura-kuran da suka yi a baya.
Sannan ya ci gaba da cewa tun yanzu an fara cece-kuce akan takarar shugaban kasa na shekara ta 2023, kabilar Yoruba na cewa lokacin su ne.

Leave a Reply