Home Home Najeriya Ta Tsayar Da Ranar Fara Kidayar Jama’ar Kasar

Najeriya Ta Tsayar Da Ranar Fara Kidayar Jama’ar Kasar

6
0

Gwamnatin tarayya, ta sanar da 3 ga watan Mayu na shekara ta 2023 a matsayin ranar da za a fara kidayar jama’a da za a shafe tsawon kwanaki 3 ana yi.

Idan dai ba a manta ba, a baya an yi ta dage shirin kidayar al’ummar Nijeriya, wanda aka tsara gudanarwa a lokuta daban-daban.

Nijeriya, wadda hasashe ke nuna cewa ta na da yawan al’umma sama da miliyan 200, har yanzu babu cikakkun alkalumman yawan jamar ta, duba da cewa shekaru 17 kenan rabon da a kirga yawan jama’a. Bayanan da hukumar kula da yawan jama’a ta fitar, ta ce a wannan karon za a gudanar da kidayar jama’ar ne a zamanance ta hanyar amfani da nau’rar komfuta.