Home Labaru Kasuwanci Shugaba Buhari Ya Jaddada Aniyar Hadin Kai Da Faransa

Shugaba Buhari Ya Jaddada Aniyar Hadin Kai Da Faransa

110
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, yayin da ya jaddada hadin kan Najeriya da kasar wajen murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Yayin da ya ziyarci fadar shugaban Faransa inda ya gana da shugaba Macron, Shugaba Buhari yace ziyarar da Macron ya kai Najeriya a shekarar 2018 ta bude kofofin ci gaba ta hanyar sana’oi, da yadda harkokin kasuwanci suka habaka, musamman kafa kungiyar zuba jari tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya yaba da rawar da shugaba Macron ya taka wajen bunkasa dangantakar kasashen biyu lokacin da ya ziyarci birnin Lagos a shekarar 2018 wadda ta bashi damar samar da yanayin da aka kafa kungiyar ‘yan kasuwa da janyo manyan ‘yan kasuwar kasashen biyu wanda shugaban kamfanin BUA Abdusamad Rabiu ke jagoranta.

Dangane da batun tsaro kuma, Buhari ya jinjinawa Faransa akan aniyar ta na tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da kuma Yankin Tafkin Chadi, wadanda suka taimaka wajen yaki da ta’addanci.

Buhari yace Najeriya da Faransa na da damar fadada dangantakar su ta hanyar tintibar juna a matakin ministoci, yayin da ya bayyana kasar a matsayin kawa abokiyar tafiya dangane da ci gaban kasashen Afirka.