Home Labaru Nadin Ministoci: Kungiyar Kwadago Ta Gargadi Shugaba Buhari A Kan Chris Ngige

Nadin Ministoci: Kungiyar Kwadago Ta Gargadi Shugaba Buhari A Kan Chris Ngige

959
0

Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya sake amincewa da Chris Ngige a ciki ministocin da zai yi aiki da su a wa’adin mulkin shin a biyu, saboda dawowar sa ba za ta haifar da komai ba illa kara janyo tabarbarewar aikin gwamnati.

Idan dai za a iya tunawa, a baya an sha kai ruwa rana tsakanin Ngige da kungiyoyin ma’aikata, inda ya sha caccaka daga kungiyoyin likitoci da na ma’aikata, sakamakon furucin da ya yi cewa ba su damu da yadda lokitoci ke ficewa zuwa wasu kasashe neman aiki ba domin akwai su birjik a fadin Nijeriya.

Nwachukwu Obidiwe

Mai Magana da yawun Ngige Nwachukwu Obidiwe, ya ce Ngige ba shi ke zaben ma’aikatar da zai rike a matsayin minista ba, kuma kafin karshen wa’adin sa na farko an sulhunta duk wasu matsalolin da ke tsakanin shi da ma’aikata.

Sakataren kungiyar kwadago ta kasa Dakta Peter Ozo-Eson, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sauya wa Ngige ma’aikatar da zai rike a matsayin minista domin kauce wa samun matsala tsakanin gwamnati da ma’aikata.

Leave a Reply