Home Labaru Zaben Kano: Kotu Ta Hana Wani Dan Kwankwasiyya Bada Shaida

Zaben Kano: Kotu Ta Hana Wani Dan Kwankwasiyya Bada Shaida

377
0

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, ta ki yarda wani shaidar masu kara Muhammad Buhari Sule ya yi bayani a gaban ta yayin zaman kotun na ranar Litinin din nan.

Kin amincewar kotun kuwa ya biyo bayan korafin da lauyan hukumar zabe Dayo Adedeji ya yi, yayin da aka kira mutumin a matsayin shaida na farko da masu kara su ka kira domin ya fara gabatar da jawabi a gaban kotun.

Lauya Adedeji ya yi korafin ne a kan sunan shaidar da aka kira a gaban kotun, inda ya ce sunan sa bai yi daidai da sunan da ke cikin takardar jerin sunayen shaidun da masu kara su ka gabatar a gaban kotun ba.

Sai dai lauyan jam’iyyar PDP Eyitayo Fatogun, ya ce bisa dokar kotun sauraren korafin zabe ta shekara ta 2011, ana boye sunan shaida ne domin bashi kariya.

Mai shari’a Halima S. Muhammad, ta ce tunda masu kara na yin amfani da harufan farko na suna domin sakaya sunan shaidun su, ta amince cewa haruffan ‘MD’ ba su yi daidai da sunan Muhammad Buhari Sule ba, don haka kotu ba za ta karbi shaidar sa ba.