Home Labaru Nadin Ministoci: An Hana Wasu Manyan Kasa Ganawa Da Buhari A London

Nadin Ministoci: An Hana Wasu Manyan Kasa Ganawa Da Buhari A London

474
0

Rahotanni na cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya zabi ya zakulo Ministocin da zai yi aiki da su ba tare da wani ya sa masa baki ba.

Wata majiya ta ce wasu daga cikin manya na kusa da shugaba Buhari da ake tunanin su ke juya Nijeriya a mulkin sa, sun tafi Birnin London amma aka hana su ganawa da shi.

Majiya ta ce an hana mutanen ganin shugaba Buhari ne kamar yadda ya bada umurni, lamarin da ya sa har yanzu babu wanda ya san shige-da-ficen shi a halin yanzu.

Ana sa ran wadanda su ka je London da nufin ganin shugaba Buhari sun je ne domin sa baki a nadin sababbin Ministocin da zai, amma an ce Minista daya kawai aka ba damar ganin shugaba Buhari.Yayin da ake jin cewa babu wanda ya san wadanda ake shirin ba mukaman Ministocin, wani daga cikin gwamnonin APC ya ce shugaban Buhari bai nemi gwamnoni su kai ma shi jerin wadanda su ke so a ba mukaman daga jihohin su ba.

Leave a Reply