Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin sa ta daura damarar ganin bayan aikin babbar gadar Neja ta biyu da ke birnin Onitsha a jihar Anambra nan ba da jimawa ba.
Buhari ya ce aikin gadar Neja wani babban ginshiki ne na bunkasar tattalin arziki a yankin Kudu maso Gabas da kuma Nijeriya baki daya.
Yayin da shugaba Buhari ke ci-gaba da hutun kwanaki goma a birnin London na kasar Birtaniya, mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi wakilce shi yayin ziyarar duba aikin gadar Neja da ya kai yankin.
Osinbajo, wanda tawagar sa ta hada da Ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana farin cikin sa tare da yaba wa kwazon Injiniyoyi masu gudanar da kwangilar aikin. Farfesa Yemi Osinbajo, ya kuma ziyarci kasuwar Akwa da ke jihar Anambra, inda ya yi wa ‘yan kasuwa masu cin gajiyar shirin TraderMoni tsokaci, cewa shirin ya kasance daya daga cikin shirye-shirye hudu na inganta jin dadin al’umma da gwamnatin su ta dabbaka.