Home Labaru Nade-Nade: Shugaba Buhari Ya Sabunta Naɗin Joseph Ari A Matsayin Shugaban ITF

Nade-Nade: Shugaba Buhari Ya Sabunta Naɗin Joseph Ari A Matsayin Shugaban ITF

225
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sake naɗa Joseph Ari a matsayin shugaban Asusun Koyar da Ayyuka ITF na tsawon shekaru huɗu.

Buhari ya amince da nadin ne a cikin wasikar da ya aike wa Ma’aikatar Cinikayya da Saka Hannun Jari a ranar Talata 16 ga watan Yuli na shekara ta 2020.

An dai fara naɗa Ari a matsayin shugaban ITF ne a shekara ta 2016, kuma naɗin sa na biyu zai fara aiki ne daga ranar 26 ga watan Satumba na shekara ta 2020.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasikar amincewa da nadin Lamido Yuguda a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da hada-hadar kudade, SEC.

Shuagaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana haka, yayin da ya ke karanto wasikar nadin Yuguda a zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata.

Shugaba Buhari, ya kuma nemi a tabbatar da naɗin wasu mutane uku, da su ka hada da Reginald C. Karausa da Ibrahim D. Biyu da Obi Joseph a matsayin kwamishinonin hukumar.