Home Labaru Nadin Kayode: ‘Yan Majalisar Sarki Biyar Sun Yi Murabus A Jihar Zamfara

Nadin Kayode: ‘Yan Majalisar Sarki Biyar Sun Yi Murabus A Jihar Zamfara

304
0

Masarautar Shinkafi da ke Jihar Zamfara, ta nada tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Nijeriya Femi Fani-Kayode a matsayin Sadaukin Shinkafi, lamarin da bai yi wa al’ummar Shinkafi dadi ba.

‘Yan majalisar Sarkin biyar dai sun yi murabus domin nuna adawa da nadin da Sarki Muhammad Makwashe ya yi wa Kayode.

Daya daga cikin ‘yan majalisar sarki kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto Dr. Tijjani Salihu ya shaida wa manema labarai cewa, ya yi murabus daga mukamin sa na ‘Uban Marayun Shinkafi’, saboda a cewar sa an ba makiyin arewacin Nijeriya sarauta, kuma mai yawan sukar sarkin Musulmi.

Alhaji Sulaiman Shu’aibu, wanda ya yi murabus daga mukamin ‘sarkin Shannun Shinkafi’, ya ce bai amince da nadin Femi Fani-Kayode a matsayin Sadaukin Shinkafi ba, saboda ya dade ya na sukar arewa da shugabannin ta.

Sarautar Sadauki sarauta ce mai daraja, wanda duk wanda ya ke da sarautar zai iya sadaukar da rayuwar sa da dukiyar sa ga al’ummar yankin, da addinin su da al’adun su da zamantakewar su, da kuma kare mutunci da muradun wadannan al’umma.