Home Labaru Nade-Nade: Rundunar Sojin Nijeriya Ta Naɗa Sabon Kakakin Ta

Nade-Nade: Rundunar Sojin Nijeriya Ta Naɗa Sabon Kakakin Ta

279
0

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da Burgediya Janar
Mohammed M. Yerima a matsayin sabon kakakin ta.

Yerima dai zai maye gurbin Burgediya Janar Sagir Musa ne,
wanda ya riƙe muƙamin shekaru biyu da su ka gabata.

Wata majiya ta ce, wannan ne na farko daga cikin sabbin naɗe-
naɗe da sabon hafsan sojin ƙasa Manjo Janar Ibrahim Attahiru
zai yi.

Brigediya Janar Yerima dai mutumin ƙaramar hukumar Bade ne
a jihar Yobe, ya kuma yi karatun kimiyyar Siyasa a jami’ar
Ahmadu Bello da ke Zaria, sannan a shekara ta 1989 ya shiga
aikin soja.