Home Labaru Martani: Shugaban ‘Yan Sanda Ya Musanta Bada Rashawa Don Tsawaita Wa’adin Sa

Martani: Shugaban ‘Yan Sanda Ya Musanta Bada Rashawa Don Tsawaita Wa’adin Sa

210
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Rundunar ‘Yan Sanda ta musanta rahotannin da ke cewa,
shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya biya
naira biliyan 2 a matsayin tsohiyar baki don tsawaita wa’adin ci-
gaba da rike mukamin sa.

A Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin ‘yan sandan Nijeriya
Frank Mba, ya bayyana rahotannin a matsayin kokarin wasu
miyagu na bata wa Muhammad Adamu masa suna.

Ya ce abin mamaki ne, ganin yadda masu yada rahoton karyar
su ka bayyana rashin murnar kara ma shi wa’adi da babban
Sifeton ya yi, a matsayin daya daga cikin hujjojin da ke tabbatar
da cewa sai da aljihun sa ya ji jiki kafin bukatar sa ta biya.

A ranar 1 ga watan Fabarairu ne, shugaba Buhari ya kara wa
shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu wa’adin ci-
gaba da rike mukamin sa, matakin da Ministan kula da ayyukan
‘yan sanda Muhammad Dingyadi ya ce an dauka, domin samun
damar zaben sabon shugaban rundunar ‘yan sandan cikin
natsuwa.