Home Labaru Na Warke Sarai Ba Tare Da Wata Matsala Ba – Tinubu

Na Warke Sarai Ba Tare Da Wata Matsala Ba – Tinubu

12
0

Jagoran jam’iyyar APC Bola Tinubu ya dawo Nijeriya, bayan ya shafe akalla tsawon watanni huɗu ya na jinya a birnin London na kasar Ingila.

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran sa ya fitar, Tinubu ya ce ya warke sarai, tare da musanta jitar-jitar da ake yaɗawa a kan rashin lafiyar tasa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an yi wa Tinubu aiki ne a gwiwar sa ta dama tare da ba shi kulawa.

A Cikin sanarwar, Tinubu ya gode wa Shugaba Buhari da gwamnoni da ‘yan majalisar yankin Arewa da na majalisar Jihar Legas bisa ziyartar sa da su ka yi a London.