Home Labaru Siyasa Na Sadaukar Da Kai Domin Yi Wa ‘Yan Najeriya Hidima – Buhari

Na Sadaukar Da Kai Domin Yi Wa ‘Yan Najeriya Hidima – Buhari

411
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi dukkanin matakan gwamnati su zage dantsen wajen sauke nauyin al’umma da ra rataya a wuyansu.

Shugaban kasa, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa mai martaba sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris, ziyarar ban girma a fadarsa dake Zaria a Kaduna.

Ya jaddada cewa, kalubale na rashin aikin yi musamman wanda ya yiwa matasa dabaibayi zai zama tarihi a Najeriya, a yayin da dukkanin matakan gwamnati za su yi wa matsalar taron dangi domin maganceta cikin gaugawa.

Buhari, ya yabawa mutanen jihar Kano da kuma Kaduna da suka bashi gudunmuwa da tarin kuri’u a lokacin zaben 2019,  ya ce yunkurin ramawa kura kyakkyawar aniyarta ya sa ya ba jihohin biyu manya kujerun ministoci bibbiyu.

Shugaban kasa ya ce jihohin Kaduna da Kano ne kadai jihohi biyu da ya ba manyan kujerun ministoci, saboda haka wannan sakayya ce ta kuri’un da suka ba jam’iyyar APC 2019.

Daga karshe, ya ce ya biya jihar Kaduna da kujerun ministan Zamantakewa da kuma ministan kudi,  jihar Kano kuma kujerar ministan tsaro da kuma ta ministan noma da raya karkara.