Home Labaru Kotu Ta Garkame Jami’an SARS A Gidan Yari A Legas

Kotu Ta Garkame Jami’an SARS A Gidan Yari A Legas

371
0

Wata kotun majistare da ke jihar  Lagas, ta bada umurnin tsare wasu jami’an tsaro na SARS 4, wadanda ake zargi da kashe wasu yan fashi biyu a gidan kurkuku.

Alkalin kotun majistaren, mai shari’a Alex Komolafe, ne ya bada umurnin a tsare su a gidan yarin Ikoyi zuwa lokacin da za a ji shawarar doka daga sashin dokokin kotun na jihar.

Mai shari’a Alex ya ki amsa rokon da mutunen 4 wadanda suka hada da Omomuyiwa Fabiyi mai shekara 42 da Solomon Olaniyi mai shekara 41 da Sunday Solomon mai shekara 41 da kuma Mukaila Aliyu mai shekara 35 suka ka yi masa.

Alkalin ya yi zargin cewa wadanda ake karan sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin yan fashi ne, inda ya ce  laifin ya sabawa sashi na 223 da 233 na dokar ta’addanci na jihar Legas, na shekara ta 2015, saboda haka ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Satumba.