Home Labaru Kasafin 2020: Shugaba Buhari Ya Aike Wa Majalisa Takardar Tsarin Kashe...

Kasafin 2020: Shugaba Buhari Ya Aike Wa Majalisa Takardar Tsarin Kashe Kudi

478
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika takardar tsarin kashe kudi da dabarun kasafin shekara ta 2020 da 2022 zuwa majalisar dattawa, lmarin da zai bada damar gabatar da kasafin shekara ta 2020.

Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Ahmad Lawan ne ya bada sanarwar, yayin zaman majalisar na na ranar Laraba.

Kudin da ake bukatar kashewa na kasafin shekara ta 2020 dai ya kama naira tiriliyan 9 da biliyan 97, sannan Jami’an gwamnati sun yi alkawarin gabatar da kasafin shekara ta 2020 da wuri.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya yi akawarin aiwatar da kasafin da wuri idan aka gabatar da shi ga ‘yan majalisar a kan lokaci.