Home Labaru Mutuwar Tolulope Arotile: Hukumar Sojin Sama Ta Bayyana Ranar Jana’iza

Mutuwar Tolulope Arotile: Hukumar Sojin Sama Ta Bayyana Ranar Jana’iza

208
0

Hukumar mayakan sojojin saman Najeriya ta ce za’a yi jana’izar matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya, Tolulope Arotile ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2020, a makabartar hafsoshin sojoji da ke unguwar Karmajiji, a Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne ya yinda ministar harkokin mata, Pauline Tallen, da  ministan labarai, Lai Mohammed, da ‘Yan majalisar dattawa suka kai gaisuwar ta’aziyya.

A jawabin da kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, da ya saki a shafin Tuwita, ya bayyana cewa za’a birneta cikin kwalliya na musamman da ake yiwa manyan hafsoshi.

Air Marshal Sadique Abubakar

Hakazalika babban hafsan Sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya karbi bakuncin wasu mambobin majalisar shugaban kasa da wasu mambobin majalisar dattawa da suka kawo masa ziyara da Hedkwatar NAF ranar Alhamis domin mika gaisuwar ta’aziyya.

Daga cikinsu akwai Ministar harkokin mata, Dame Tallen Pauline da kuma Ministan Labarai da al’adi, Alhaji Lai Mohammed.” “Hakalika akwai tawagar mambobin majalisar dokokin tarayya kimanin mutane 20 karkshin jagorancin shugaban kwamitin hukumar Soji a majalisar dattawa, Sanata Bala Ibn-Na’Allah.