Home Labaru Almundahana: Joy Nunieh Ta Fayyacewa Majalisar Tarayya Gaskiya Kan Badakalar NDDC

Almundahana: Joy Nunieh Ta Fayyacewa Majalisar Tarayya Gaskiya Kan Badakalar NDDC

179
0
Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bagi A Kasafin NDDC
Majalisa Ta Jefa Kwangilolin Bagi A Kasafin NDDC

Tsohuwar mukaddashiyar daraktan hukumar bunkasa Niger Delta, Joy Nunieh, ta fayyace gaskiya gaban kwamitin majalisar wakilai da ke bincike kan badakalar da aka tafka a hukumar NDDC na karkatar da wasu kudade.

Joy Nunieh, Tsohuwar mukaddashiyar daraktan hukumar bunkasa Niger Delta

Binciken da ake yi na badakalar hukumar NDDC ya kara daukar zafi inda jami’an rundunar ‘yan sanda suka mamaye gidan Nunieh da ke Fatakwa a jihar Rivers..

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ya hana jami’an ‘yan sandan awon gaba da Nunieh, ya bukaci shugaban rundunar yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, da ya binciki lamarin.

Akwai zargin da ake yi na cewar ‘yan sandan sun mamaye gidan Nunieh,  ne domin hana ta barin Fatakwal zuwa Abuja inda za ta fayyace gaskiya gaban kwamitin binciken.

Manyan jami’an hukumar NDDC, da suka bayyana gaban kwamitin binciken sa sun fice daga zauren inda suka bukaci shugaban kwamitin, Mr Olubunmi Tunji-Ojo ya yi murabus.

A baya bayan nan, tsohuwar mukaddashin daraktar hukumar NDDC Joy Nunieh, ta zargi ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio, da damfarar kudin hukumar NDDC.