Home Labaru Gargadi: Ba Zan Lamunci Cin Zarafin ‘Yan Majalisar Tarayyata Ba -Buhari

Gargadi: Ba Zan Lamunci Cin Zarafin ‘Yan Majalisar Tarayyata Ba -Buhari

302
0
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare
Kasafin Kudi: Buhari Ya Dakatar Da Ministoci Daga Zuwa Kashashen Ketare

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ja kunnen dukkan wadanda ya nada a kan cewa ba zai lamunci rashin da’a ga majalisar tarayyar sa ba.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya fitar, ta ce  shugaban kasa ya ja kunnen bayan karbar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan za a iya tunawa majalisar dattawa da karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo, sun yi kaca-kaca a kan bayanin ayyuka dubu dari 7 da 74,  a yayin bayani game da kasafin aikin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ministoci, shugabannin sashe da cibiyoyi  su kama kansu domin ba zai amince ana cin zarafin ‘yan majalisar tarayyar sa ba.

Ana shawartar dukkannin ministoci da shugabannin sassa da cibiyoyi a kowanne lokaci su dinga kama kansu ta yadda ba za su rika cin fuskar kowa ba.