Home Labaru Kiwon Lafiya Mai Coronavirus A Ekiti Ya Warke

Mai Coronavirus A Ekiti Ya Warke

345
0

Mutumin da ya kamu cutar Coronavirus ya warke a jihar Ekiti.

An sallami matashin mai shekara 37 daga cibiyar killace masu cutar coronavirus a jihar, inda aka yi jinyarsa tun ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.

A ranar Talata ne aka sallami mutumin bayan ya murmure kuma sakamakon gwajin cutr da aka yi masa ya tabbatar da cewa cutar ta rabu da shi.

Kawo yanzo mutumin matashin shi ne kadai aka tabbatar ya taba kamuwa da cutar da jihar.

Kwamishinar Lafiyan jihar Ekiti, Dr. Mojisola Yaya-Kolade, ce ta tabbatar da haka a ranar Talata.

Ta ce mutum 41 ne sun killace kansu a fadin jihar Ekiti, bayan mu’mala da suka yi da mutumin da yanzu ya warke daga cutar.

Kwamishinar ta ce dukkansu sun samu cikakkiyar kulawar da ta dace daga jami’an lafiya.

A ranar 14 ga Afrilu ne wa’adin killace kan da mutanen suka yi zai kare, kafin su ci gaba da hulda da jama’a kamar yadda aka saba.