Home Labaru Kiwon Lafiya Mutum Na Uku Ya Harbu Da COVID-19 A Bauchi

Mutum Na Uku Ya Harbu Da COVID-19 A Bauchi

408
0
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a fadin jihar Kano, kawo yanzu
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a fadin jihar Kano, kawo yanzu

Mutum na uku ya kamu da cutar coronavirus a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Mataimakin gwaman jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya tabbatar da haka a ranar Talata.

Baba Tela wanda shi ke jagorantar Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus a jihar Bauchi ya ce, wanda ya harbu da cutar a baya-bayan nan, namiji ne dan shekara 55.

Kawo yanzu, mutum 3 ne hukumomin jihar suka tabbatar na dauke da cutar coronavirus a jihar Bauchi.

Gwamnan jihar Bala Muhammad shi ne wanda ya fara kamuwa da COVID-19 a jihar, kuma tuni ya killace kansa.

Gwamnan ya samar da kamuwarsa da cutar ne, ‘yan kwanaki bayan dawowarsa daga kasar waje.