Home Labaru Kiwon Lafiya Yaki Da COVID-19: ‘Yan Majalisa Sun Yafe Albashin Wata 2

Yaki Da COVID-19: ‘Yan Majalisa Sun Yafe Albashin Wata 2

378
0
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace

‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun ba da albashinsu na wata biyu domin a yaki annobar Coronavirus.

‘Yan Majalisar sun yafe albashinsu na wata biyu kacokan a matsayin tallafi domin a yaki annobar da ke addabar kasashe.

‘Yan Majalisar za kuma su ci gaba da tallafawa ta hanyoyi daban daban a yaki cutar, baya ga sallama albashinsu na wata biyu ga gidauniyar yaki da cutar.

Da yake bayyana hana, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce yaki da COVID-19 nauyi da ya rataya a kan duk wanda ke da hali gwargwadon iko, domin ganin kawar da cutar.

Sallama albashin ‘yan Majalisar wakilan na zuwa ne washegarin ranar da ‘yan Majalisar Dattawa suka sanar da bayar da rabin albashinsu a matsayin tallafi, har sai an shawo kan annobar.