Gwamnatin Tarayya ta rage kasafin kudin Majalisar Tarayya na shekarar 2020 da naira biliyan 25.6.
Gwamnatin ta kuma dakatar da kwaskwarima da kammala ginin majalisar da zai lakume naira biliyan 37.
Mummunar faduwar farashin danyen mai ya tilasta wa gwamntin rage kasafinta kashi 20 daga kasafinta na shekarar 2020, kamar yadda Mai Tsawatarwar Majalisar Dattawa, Muhammad Tahir Monguno, ya tabbatar wa majiyarmu.
Dan majalisar ya ce ragin kashi 20 din zai shafi kasafin bangaren zartarwa da bangaren dokoki da bangren shari’a. Kuma kowane bangare na sake nazarin kasafinda domin hakura da wasu ayyuka da aka ware wa kudade a baya.
Najeriya ta rage yawan kasafinta na 2020 daga naira tiriliyan 10.3 zuwa naira tiriliyan 8, biyo bayan illar da annobar coronavirus ta yi wa tattalin arzikin duniya, wanda ya karya farashin gangar mai zuwa kasa da dala 52.
Shaidu a majalisar na cewa majalisar tarayyar na jiran bangaren zartaswa ya mika masa kasafin kudin da aka yi wa gyaran fuskaa domin amincewa.