
Hukumomi a Nijeriya, sun ce sama da mutane dubu tamanin ne su ka shigo daga kasashen waje a matsayin ‘yan gudun hijira.
Shugabar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Nijeriya Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ta bayyana haka, yayin da ake bikin tunawa da Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya.
Hajiya Imaan ta kara da cewa, mutanen da su ka shigo Nijeriya sun fito ne daga kasashe talatin da hudu, kuma wadanda su ka yi rajista kusan dubu tamanin da hudu ne.
Ta ce Mutanen da su ka fi shigowa Nijeriya sun fito ne daga Kudancin Kamaru saboda ana rikici a yankin Ambazonia.
Hajiya Imaan ta cigaba da cewa, gwamnatin Nijeriya ta na ware makudan kudade domin tallafa wa ‘yan gudun hijirar kamar yadda dokokin kasashen duniya su ka bukata, kuma ‘yan gudun hijirar su na da zabi uku, ko dai su cigaba da zama a Nijeriya, ko kuma su koma kasashen su idan sun gamsu da yanayin da ake ciki a can, ko kuma Najeriya ta kai su wasu kasashen.













































