Home Labarai Isah Ashiru Yay i Wa El-Rufa’i Raddi A Kan Korar Ma’aikatan Jihar Kaduna

Isah Ashiru Yay i Wa El-Rufa’i Raddi A Kan Korar Ma’aikatan Jihar Kaduna

392
0

Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isah Ashiru Kudan, ya yi kira ga gwamnan Nasir El-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da ya ke yi a jihar.

Idan dai ba a manta ba, gwamnatin El-Rufai ta kori malaman makarantun firamare, ciki har da shugaban kungiyar malamai ta kasa wanda ɗan asalin jihar Kaduna ne.

Isah Ashiru ya soki hakan a cikin wani gajeren sako da ya fitar, inda ya ce a wannan lokaci da talaka ke hannu-baka-hannu- kwarya bai kamata a ce an gallaza ma shi irin wannan azaba ta korar aiki da rana tsaka ba.

Ya ce ana fama da talauci da wahalhalun rayuwa sai kuma a wayi gari ɗan aikin da talaka ke samun abinci an kore shi.

A karshe ya yi kira ga gwamna El-Rufa’i ya dakatar da korar ma’aikatan da ya ke cigaba da yi, domin a halin yanzu al’ummar jihar Kaduna su na fuskantar matsalolin rayuwa dabam dabam, don haka idan ba a tallafa masu ba to bai kamata a ce ana raba su da ayyukan da su ka dogara da su domin ciyar da iyalan su
ba.

Leave a Reply