Home Labarai Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Kaduna, Sun Sace Mutane...

Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari Kaduna, Sun Sace Mutane 36

43
0

Akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su, a wani hari da ‘yan bindiga su ka kai wasu kauyuka hudu da ke karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Mazauna kauyukan ne su ka bayyana haka, yayin wata ganawa da jami’an tsaro, inda su ka ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwar su, domin ba za su iya zuwa gonakin su ba don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.

Mutanen sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa sansanin sojoji a Kajuru, domin ita kadai ce hanyar da za a magance matsalar tsaro.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun shiga ne a kan Babura, inda su ka kara sace babura daga mutanen kauyen domin su tafi da wasu mutane, yayin da su ka kashe wasu daga cikin mutanen kauyen da su ka yi kokarin dakile harin tare da jikkata wasu.