Home Labaru Mutum 13 Sun Mutu A Jihar Ogun Ranar Kirsimeti

Mutum 13 Sun Mutu A Jihar Ogun Ranar Kirsimeti

35
0

Mutum 13 sun rasu yayin da wasu 19 suka ji raunuka daban-daban a wasu hatsarin mota biyu da suka auku ranar Kirsimeti a Jihar Ogun.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust hatsarin farko ya ritsa da wata motar bas ƙirar Mercedes Benz ce a kan Titin Sagamu zuwa Benin, inda mutum bakwai suka mutu sannan bakwai suka jikkata.

Motar bas ɗin ta taso ne daga Ojuelegba na Jihar Legas, kuma hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 12:20 na daren Asabar ba tare da ya ritsa da wata motar ba.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗurra ta Jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce hatsarin ya ritsa da mutum 63, maza 40, manyan mata 15, yara maza biyar da kuma yara mata uku.

Ta ƙara da cewa hatsari na biyu ya faru a kan gadar Long Bridge da ke kan Titin Lagos zuwa Ibadan, inda mutum shida suka rasa rayukan su tare da jikkata 12.