Home Labaru An Fitar Da Tawagar Super Eagles Da Za Ta Wakilci Najeriya

An Fitar Da Tawagar Super Eagles Da Za Ta Wakilci Najeriya

51
0

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ya bayyana sunan mutum 28 da za su wakilci Najeriya a gasar Kofin Ƙasashen Afirka na 2022 da Kamaru za ta karɓi baƙunci.

Kyaftin Ahmed Musa da kuma tauraron ɗan wasan tsakiya na Leicester City Wilfred Ndidi na cikin tawagar.

Kociya Austin Eguavoen zai jagoranci Najeriya da ta ɗauki kofin sau uku a wasannin da za ta fafata da Egypt mai kambin gasar biyar da Sudan da Guinea Bissau a rukunin D, wasan da Za ta fara karawa da Egypt ranar 11 ga watan Janairu.

Ƙasashe 24 ne za su fafata a gasar wadda za a gudanar daga 9 ga Janairu zuwa 6 ga watan Fabarairun 2022 a ƙasar Kamaru.

Cikakkiyar tawagar Najeriyan su ne.

Gola: Francis Uzoho, John Noble, Daniel Akpeyi, Maduka Okoye.

‘Yan baya:  Chidozie Awaziem, Kenneth Omeruo, Leon Balogun, William Ekong, Olaoluwa Aina, Jamilu Collins, Abdullahi Shehu, Zaidu Sanusi, Olisa Ndah.

‘Yan tsakiya: Frank Onyeka, Joseph Ayodele-Aribo, Wilfred Ndidi, Chidera Ejuke, Kelechi Nwakali.

‘Yan gaba: Ahmed Musa, Samuel Chukwueze, Victor Osimhen, Moses Simon, Sadiq Umar, Taiwo Awoniyi, Odion Jude Ighalo, Alex Iwobi, Kelechi Iheanacho, Emmanuel Dennis.