Home Ilimi Mutane 8,372 Aka Kashe Kuma Satar Mutane Ta Ƙaru Cikin 2021 a...

Mutane 8,372 Aka Kashe Kuma Satar Mutane Ta Ƙaru Cikin 2021 a Nijeriya – Rahoto

174
0

Aƙalla Mutum dubu 8 da 372 aka kashe a fadin Nijeriya cikin shekara ta 2021 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga kamar yadda wani rahoto da aka fitar ya nuna.

Binciken dai ya gano cewa, matsalar garkuwa da mutane ta ƙaru
da kashi 58 cikin 100 daga watan Oktoba zuwa Disamba na
shekara ta 2021, inda aka samu rahoton garkuwa da mutane har
sau 574.

Rahoton na kamfanin Beacon Consulting mai sharhi a kan
al’amurran tsaro, ya ce an kashe aƙalla mutane dubu 1 da 516 a
cikin watanni ukun ƙarshe na shekara ta 2021.

Yankin arewa maso yammacin Nijeriya ne ke da adadi mafi
yawa na dubu 3 da 51 da aka kashe a cikin watanni ukun, sai
kuma yankin arewa maso gabas da ke da mutane dubu 1 da 895,
yayin da arewa ta tsakiya ke da dubu 1 da 684.

Rahoton ya cigaba da cewa, yankin kudu maso gabas ya na da
mutane 853, sai kuma yankin kudu maso kudu da ke da adadin
mutane 448, yayin da yankin kudu maso yamma ke da 441.