Allah Ya yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo Alao Akala rasuwa a yana da shekara 71 a duniya.
Marigayin dai ya taɓa rike mukamin gwamnan jihar Oyo daga
shekara ta 2007 zuwa 2011.
Alao-Akala dai ɗan asalin ƙaramar hukumar Ogbomoso ta arewa
ne, wanda kafin ya zama gwamna sai da ya yi mataimakin
gwamna a tsakanin watan Mayu na shekara ta 2003 zuwa
Janairu na shekara ta 2006 a ƙrƙashin jam’iyyar PDP.
A shekara ta 2014 ne tsohon gwamnan ya koma jam’iyyar
Labour, bisa hujjar cewa ana gudanar da abubuwan da ba su
dace ba a tsohuwar jam’iyyar sa.
A shekara ta 2015 ne, Alao-Akala ya sake tsayawa takarar
gwamna a karkashin jam’iyyar Labour amma bai yi nasara ba,
sannan ya sake tsayawa takarar gwamna a ƙrƙashin jam’iyyar
ADP a shekara ta 2019.














































