Home Coronavirus Mutane 1,273 Ne Suka Kamu Da Cutar Coronavirus A Nijeriya-NCDC

Mutane 1,273 Ne Suka Kamu Da Cutar Coronavirus A Nijeriya-NCDC

299
0
Mutane 1,273 Ne Suka Kamu Da Cutar Coronavirus A Nijeriya-NCDC
Mutane 1,273 Ne Suka Kamu Da Cutar Coronavirus A Nijeriya-NCDC

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce an samu karin mutane 91 da su ka kamu da cutar Coronavirus a Nijeriya.

Sabbin alkaluman sun nuna cewa jihar Legas na da adadin mutum 43 da suka sake da cutar sai jihar Sakkwato da ke da mutane takwas, lamarin da ya sa jihar ke da mutane 10 da da suka kamun da cutar.

Haka kuma NCDC ta tabbatar da bullar cutar a karon farko a jihohin Kebbi da Ebonyi, da kuma Bayelsa, inda kowacce jiha ke da mutum guda-guda.

Alkalummar cibiyar sun kuma tabbatar da mutuwar mutane biyar a ranar Lahadi, wanda hakan ya bada adadin mutane 40 n da suka mutu a Nijeriya.

Kawo yanzu dai, annobar Coronavirus ta ratsa jihohi jihohi 31 a Nijeriya, baya ga babban birnin tarayya Abuja.