Home Labaru Kiwon Lafiya Covid-19: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Jihar Kano-Ganduje

Covid-19: Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Jihar Kano-Ganduje

503
0
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar Coronavirus ya yi watsi da jihar Kano duk da mawuyacin halin da jihar ta shiga.

Gandunje ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, tare da cewa halin da ake cikin yanzu a jihar kano na da ban tsoro.

Gwamna Ganduje ya ce, babban abinda aka dogara da shi wajen dakile cutar a jihar shine, yin gwaji wanda shima sai an shafe kwanaki biyar zuwa shida da daukar samufurin jinin mutane ba tare da sanin matsayin su ba.

Haka kuma, Ganduje ya kara da cewa babban daraktar cibiyar dakile yawuwar cututtuka NCDC ya zo jihar Kano, amma tun da ya tafi ba mu sake jin duriyar sa ba, zargin da kwamin yaki da cutar na shugaban kasa ya musanta.

Ganduje ya ce, baya ga karancin cibiyoyin gwajin cutar, jihar kano ba ta da isassun kayayyakin gwajin cutar, musamman wadanda gwamnatin tarayya ce kadai ke samar da su, kana ba su samun taimako da hadin kai daga kwamitin shugaban kasa.

A karshe Ganduje ya ce ya yi magana da jami’an gwamnatin tarayya a matakai daban-daban, amma har yanzu babu wani sakamako.