Home Home Muna Bukatar Gwamnatin Da Ta San Yadda Ake Mulki – Obasanjo

Muna Bukatar Gwamnatin Da Ta San Yadda Ake Mulki – Obasanjo

22
0
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Nijeriya ta na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da harkokin mulki.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Nijeriya ta na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da harkokin mulki.

Obasanjo ya bayyana haka ne, a wajen taron bikin cikar makarantar Kings college da ke Legas shekaru 113 da kafuwa, inda ya ce kishin kasa shi ne tubalin jagorancin al’umma, kuma raunin jagoranci shi ke haifar da rashin adalci.

Ya ce ba za mu yarda da kan mu ba bayan mun rasa kwarin gwiwa, domin a duk inda aka rasa kwarin gwiwwa lallai an rasa hadin kai’.

Tsohon shugaban kasar, ya ce iIdan babu kyakkyawar manufa babu yadda za a iya sanin makomar matasa, don haka dole da farko jama’a su sanya kishin kasa a ran su kafin duk wani abin da zai biyo baya.