Home Home Gwamnatin Tarayya Na Neman Wadabda Za Ta Jinginarwa Layukan Dogo

Gwamnatin Tarayya Na Neman Wadabda Za Ta Jinginarwa Layukan Dogo

26
0
Gwamnatin Tarayya ta fara cigiyar ‘yan kasuwar da za su zuba jari, domin ta jinginar da titunan jirgin kasa na Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna da kuma na Itakpe zuwa Warri.

Gwamnatin Tarayya ta fara cigiyar ‘yan kasuwar da za su zuba jari, domin ta jinginar da titunan jirgin kasa na Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna da kuma na Itakpe zuwa Warri.

Ministan Sufuri Mu’azu Jaji Sambo ya bayyana haka, a wani jawabi da ya gabatar a kan samar da kudaden tafiyar da harkokin sufurin Nijeriya, yayin wani taron hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.

Mu’azu Jaji Sambo, ya ce Hukumar Kula da Sufurin Jiragen kasa ta Nijeriya NRC, za ta gudanar da aikin tare da masu gudanarwa da masu aiki daban-daban.

Ya ce Sauran damarmakin sun hada da garanbawul ga sabon layin dogo da aka gina daga Abuja zuwa Kaduna mai nisan kilomita 187 da rabi, da na Warri zuwa Itakpe zuwa Ajaokuta mai nisan kilomita 326, da kuma na Legas zuwa Ibadan mai kilomita 118.

Ministan ya kara da cewa, akwai wata damar zuba jari a bangaren tashoshin ruwa, musamman ma na Badagry da Legas da Ibaka da Akwa Ibom da sauran tashoshin ruwa da ake shirin samarwa.