Home Home An Kama “Rikakken Mai Satar Mutane” Da Ke Fariya Da Kudinsa

An Kama “Rikakken Mai Satar Mutane” Da Ke Fariya Da Kudinsa

23
0
Jami’an ‘yan sanda sun kama wani da ake zargin rikakken mai satar mutane ne saboda fariyar da ya ke nunawa da dukiyar sa a shafukan sada zumunta.

Jami’an ‘yan sanda sun kama wani da ake zargin rikakken mai satar mutane ne saboda fariyar da ya ke nunawa da dukiyar sa a shafukan sada zumunta.

Da dama Mutane sun san John Lyon a matsayin ma’aikacin banki, wanda a kullum rubuce-rubucen da ya ke wallafawa ya na shawartar mutane su yi aiki tukuru kuma su kasance cikin aminci da taka-tsantsan.

Mai magana da yawun yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Bayelsa Asimi Butswat, ya shaida wa manema labarai cewa tuni John Lyon ya na tsare a hannun su.

Asimi Butswat ya ce, tuni an maida mutumin da ake zargin zuwa Bayelsa bayan an kama shi a Abuja,

Kakakin ‘yan sandan, ya ce duk lokacin da su John Lyon su ka samu kudin su na zuwa Abuja ne su yi ta rayuwar kece-raini.

Hukumomi sun ce, satar mutane domin neman kudin fansa akalla goma ake zargin gungun John Lyon da aikatawa.