Home Labaru Hana Auren Jinsi: Kungiyar CAN Ta Jinjina Wa Shugaba Muhammadu Buhari

Hana Auren Jinsi: Kungiyar CAN Ta Jinjina Wa Shugaba Muhammadu Buhari

368
0

Kungiyar kiristoci ta Nijeriya CAN, ta jinjina wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kan tirjiyar da ta nuna wajen yaki da kokarin kakaba wa ‘yan Nijeriya auren jinsi da turawa ke yunkurin yi.

Shugaban kungiyar Samson Ayokunle ya bayyana haka, inda ya ce kokarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na haramta auren jinsi da kuma sauya halitta daga namiji zuwa mace ko mace zuwa namiji abin a yaba mata ne.

Ayokunle ya bayyana haka ne ta bakin kaakakin sa Adebyao Oladeji a Abuja, inda ya koka da yadda badala ke kara wanzuwa a Nijeriya, ya na mai bayyana sauya halitta a matsayin haramtaccen lamari.

Ya kuma jinjina wa shugaban hukumar ci-gaban al’adun gargajiya ta Nijeriya Otunba Olusegun Runsewa, bisa yadda ya ke yaki da miyagun ayyukan madigo da luwadi da sauya halitta a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ya ce su na da yakinin duk wani mai hankali da kungiyoyi masu zaman kan su za su hada kai da gwamnati domin kawar da wadannan miyagun ayyuka daga Nijeriya, saboda kundin tsarin mulkin da dokokin kasar nan ba su san luwadi da madigo da sauya halitta ba kuma haramun ne a addinin mu da al’adun mu.