Home Labaru Mun Kubutar Da Mutane 300 Ba Tare Da Biyan Ko Sisi Ba...

Mun Kubutar Da Mutane 300 Ba Tare Da Biyan Ko Sisi Ba – Matawalle

277
0

Gwamnan jihar Zamfara Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya ce gwamnatin sa ta kubutar da sama da mutane 300 da ‘yan bindiga ke rike da su a jihar ba tare da biyan kudin fansa ba.

Matawalle ya bayyana haka ne, yayin da ya ke sa hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da wani bankin kasuwanci a kan harkokin da su ka shafi hakar ma’adanai da noma da albarkatun ruwa da ayyukan raya kasa.

Ya ce jihar Zamfara ta na fuskantar kalubale masu yawa kafin ya zama gwamna, amma cikin wata guda kacal Allah ya ba su sa’ar warware wasu daga cikin kalubalen da jihar ke fuskanta.

Matawalle ya kara da cewa, ta hanya sulhun da su ke yi da ‘yan bindigar, yanzu haka sun yi nasarar kubutar da mutane sama da 300 da aka yi garkuwa da su, don haka ya ce su na bada tabbacin cewa masu saka hannun jari za su iya zuwa jihar Zamfara su yi kasuwanci ba tare da fargabar rashin tsaro ba.