Home Labaru Mun Gamsu Da Matakan Tsaro Da Gwamnati Ke Dauka – Dattawan Arewa

Mun Gamsu Da Matakan Tsaro Da Gwamnati Ke Dauka – Dattawan Arewa

20
0

Kungiyar dattawan Arewa, ta musanta rahotannin da ke cewa ta kushe matakan da gwamnati ta dauka na rufe kasuwanni da yanke hanyoyin sadarwa, domin yaki da ta’addanci a jihohin Arewa maso yamma.

Da yake zantawa da manema labarai, mai magana da yawun kungiyar Hakeem Baba Ahmed, ya ce sun fi kowa farin ciki da daukar wadannan matakan, sai dai sun bada shawara a kan yadda ya kamata a yi domin kada su kara haifar da kunci ga al’ummar jihohin.

Ya ce, matakan da aka dauka suna da muhimmanci, don haka suka goyon bayansu, amma suna fatan matakan ba za su dauki lokaci mai tsawo ba.

Baba Ahmed ya kara da cewa, dole ne a sa ido domin an daura wa mutane takunkumi, sannan gwamnati ta kara nata saboda matsalar rashin tsaro.

A karshe ya bukaci gwamnatin tarayya ta shigo da karfinta domin gano ‘yan ta’addan a duk inda suke don a hukunta su, saboda kada a bar mutane cikin wahala da rashin tsira ta kowane bangare.