Home Labaru Juyin Mulkin Guinea: Sojoji Sun Saki Fursunonin Siyasa

Juyin Mulkin Guinea: Sojoji Sun Saki Fursunonin Siyasa

17
0

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea ranar Lahadi sun saki aƙalla fursunonin siyasa 79 da gwamnatin da suka kifar. Yan siyasar na daga cikin kason farko na mutun 400 da tumɓukakken Shugaba Alpha Conde ya kama a lokacin zanga zangar da ta biyo bayan babban zaɓen da a ka yi bara.

Wannan na zuwa ne yayin da Shugabannin ƙungiyar raya tattalin arzikin yankin Afrika ta Yamma wato ECOWAS, ke shirin zama a yau Laraba don tattauna batun juyin mulkin a Guinea da kuma maido da mulkin farar hula a Mali.

An ruwaito cewa tun a ranar Talata ne jerin motocin sojojin su ka isa gidajen yarin da fursunonin ke tsare inda suka kwaso kason farko.

Sakin fursunonin kan iya zama matakin farko na samar wa sabuwar gwamnatin sojin a ƙarƙashin Laftanar Kanar Mamady Doumbouya martaba ga idon jama’a.

Tun bayan juyin mulkin na ranar Lahadi Kanar Doumbouya ya yi alƙawarin samar da gwamnatin riƙo da za ta haɗa da sojoji da fararen hula, wadda kuma za ta samar da mulki nagari da kuma ci gaban tattalin arzikin Guinea.

Sai dai kuma bai faɗi lokacin da za su kafa gwamnatin ba, ballantana sadda za a sake sabon zaɓe.