Home Labaru Bata Gari Sun Kona Jami’an Yan Sanda A Jihar Delta

Bata Gari Sun Kona Jami’an Yan Sanda A Jihar Delta

12
0

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wasu jami’an ‘yan Sanda guda 3 tare da kona gawarwakinsu a Jihar Delta.

Rahotanni sun ce, an kashe jami’an ‘yan Sandan ne a lokacin da suke wurin binciken ababan hawa a kan hanyar Obeti zuwa Oliogo da ke karamar hukumar Ukwuani.

Wata majiya ta ce, bata garin sun yi wa jami’an ‘yan Sandan kwantan-bauna, inda bayan sun harbe su suka kuma kona su a cikin motar su kirar Toyota Sienna.

Wani shaidan gani da ido ya ce, an kona gawarwakin jami’an yadda ba za a iya gane su ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Jihar Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami’an ‘yan Sanda da soji na fuskantar irin wadannan hare-haren a yankin kudu maso gabas, wanda ake zargin ‘ya’yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB.

Akalla sama da jami’an ‘yan Sanda 150 aka kashe a yankin kudu maso gabashin Nijeriya a wannan shekarar, tare da sace wasu makaman su.