Home Labaru Ilimi Karatun Bogi: Hukumar NECO Ta Kori Ma’aikatan Ta 70

Karatun Bogi: Hukumar NECO Ta Kori Ma’aikatan Ta 70

519
0
Hukumar Kula Da Jarabawar Kammala Karatun Sakandare A Nijeriya NECO
Hukumar Kula Da Jarabawar Kammala Karatun Sakandare A Nijeriya NECO

Hukumar Kula da jarabawar kammala karatun Sakandare a Nijeriya NECO, ta sanar da korar ma’aikatan ta 70 saboda mallakar takardun kammala karatu na bogi.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar Azeez Sani, ya ce an kori ma’aikatan ne bayan wani kwamitin tantance takardun ma’aikata ya kammala aikin sa da ya hada da gayyatar wadanda ake zargi domin kare kan su.

Ya ce wasu daga cikin ma’aikatan da kan su su ka shaida wa kwamitin cewa takardun su na bogi ne, yayin da kwamitin ya tuntubi wasu makarantun da ma’aikatan su ka ce sun kammala, wadanda su ka musanta takardun shaidar da suka gabatar.

Jami’in ya ce bayan kammala binciken, kwamitin ya mika rahoton sa ga hukumar, wadda ta gabatar wa shugabannin gudanarwar ta domin nazari a kai.

Sani ya kara da cewa, taron hukumar gudanarwar na 17 ya amince da korar ma’aikatan 70, wadanda ya bayyana su a matsayin matakin farko.

Leave a Reply