Home Labaru Muhammad Salah Zai Goge Tarihin Da Didier Drogba Ya Kafa A Gasar...

Muhammad Salah Zai Goge Tarihin Da Didier Drogba Ya Kafa A Gasar Firimiya

10
0

Sadio Mane shi ne ɗan wasan Afrika na uku da ya ci kwallo 100 a gasar Premier League bayan Didier Drogb da Mohamed Salah.

Kwallaye uku Roberto Firmino ya ci a wasan da Liverpool ta lallasa Watford, wasan farko da Claudio Ranieri ya jagoranci kungiyar a gidan ta.

Liverpool dai ta doke Watford ne ci 5-0.

Mohamed Salah ne ya ci ƙwallo ta hudu da ta kayatar a wasan bayan ya yanke masu tsaron baya kafin ya jefa kwallon a ragar Watford.

Yanzun Salah ya yi kafada da kafada da Didier Drogba a matsayin ƴan wasan Afrika da suka fi cin ƙwallaye a gasar Premier League da ƙwallo 104.

Firmino ne ya rufe da ƙwallo ta biyar ana dab da hure wasan, karon farko da ya ci kwallo uku rigis tun watan Disamban 2018.

Har yanzu ba a doke Liverpool ba a bana. Yanzu ta ɗare tebur kafin Chelsea ta kai wa Brentford ziyara.