Home Labaru Matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

11
0

Allah Ya yi wa matar babban malamin addinin musulunci nan, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wato Hajiya Aminatu Bintu, rasuwa.

Marigayiya Hajiya Aminatu Bintu, ita ce mahaifiyar Birgediya Janar Abdulkadir Gumi, kuma ta rasu ne a ranar Asabar da safe a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna, tana da shekara 88.

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi shi ne mahaifin Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi da dan’uwan sa, Janar Abdulkadir Gumi.

Tuni aka yi jana’izar ta bayan Sallar La’asar a Masallacin marigayi Sheikh Abubakar Mahmdu Gumi, inda yanzu Dokta Ahmad Gumi yake da zama a Kaduna, bisa tsarin addinin musulunci.