Home Labaru Mu Daina Zargin Kowa Game Da Matsalar Tsaro A Nijeriya – Obasanjo

Mu Daina Zargin Kowa Game Da Matsalar Tsaro A Nijeriya – Obasanjo

550
0
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa
Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya gargadi ‘yan Nijeriya su dawo daga rakiyar zargin shugabanni game da ta’azzarar matsalar rashin tsaro da a ke fuskanta ba dare ba rana.

Obasanjo, ya ce magance matsalar tsaro a Nijeriya hakki ne da ya rataya a wuyan kowa, maimakon ci-gaba da zargin gazawar shugabanni.

Tsohon shugaban kasar, ya bukaci ‘yan Nijeriya su mike tsaye wajen yakar ta’addancin masu garkuwa da mutane, da barayin shanu da sauran kalubalen rashin tsaro da su ka yi wa Nijeriya dabaibayi.

Furucin Obasanjo dai ya na zuwa ne, yayin ganawa da shugabannin kungiyoyin Fulani a harabar gidan sa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun, inda ya ganawar ta gudana ne domin kulla dabarun magance annobar ta’addanci da rikicin makiyaya da manoma da sauran kalubalen rashin tsaro.

A karshe tsohon shugaban kasar, ya bukaci a daina zargin wasu kabilu da laifin jefa Nijeriya cikin matsalar rashin tsaro da ta ke fuskanta a yanzu.