Home Labaru Magoya Buhari Sun Shirya Tarwatsa Zanga-Zangar Juyin Juya Hali

Magoya Buhari Sun Shirya Tarwatsa Zanga-Zangar Juyin Juya Hali

755
0

Rahotanni na cewa, an hango wata mota kirar Bas cike da magoya bayan gwamnati a Unity Fountain da ke Abuja, inda su ke shirin dakile zanga-zangar da ake shirin yi ta juyin-juya-hali.

Tuni dai an fara zanga-zangar a birnin Lagos, amma a Abuja ruwan sama mai karfi da aka yi ya janyo wa lamarin cikas, sai dai wadanda su ka shirya gangamin sun ce lallai za a gudanar da zanga-zangar babu fashi.

Yayin da masu zanga-zangar su ka fara taruwa a hankali a wani waje da ba su son bayyanawa har sai sun shirya fara gangamin, wasu mutane da su ka shirya hana ganganmin sun dade da taruwa a cibiyar birnin.

Da misalin karfe 10:30 na safe, wata majiya ta ce ta hango motocin Bas biyu cike da magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari a Unity Fountain a cikin shirin ko-ta-kwana.