Home Labaru Kishin Kasa: Buhari Ya Jinjina Wa ‘Yan Nijeriya Bisa Kaurace Wa Zanga-Zangar...

Kishin Kasa: Buhari Ya Jinjina Wa ‘Yan Nijeriya Bisa Kaurace Wa Zanga-Zangar Juyin-Juya-Hali

341
0
Shugaba Muhammadu-Buhari-2
Shugaba Muhammadu-Buhari-2

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jinjina wa daukacin al’ummomin Nijeriya da su ka kaurace wa kiraye-kirayen da aka rika yi a shafukan sada zumun ta, cewa su fito zanga-zangar juyin-juya hali, inda su ka maida hankali ga harkokin gaban su.

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu

Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Ya ce shugaba Buhari ya ji dadin goyon bayan da aka ba tafiyar dimokradiyya a Nijeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, duk da akwai daruruwan mutanen da su ka shiga gangamin, sun yi hakan ne domin cimma muradun kawukan su ba da nufin ci-gaban kasa ba.