Home Labaru Motar Fasinja Ta Afka Cikin Kogi A Legas

Motar Fasinja Ta Afka Cikin Kogi A Legas

34
0

 

Ana fargabar mutum ɗaya ya rasu a Jihar Legas yayin da wata motar bas ta fasinja ta afka cikin kogi ranar Litinin.

Waɗanda lamarin ya faru a kan idon su sun ce ana tunanin direban ya kasa sarrafa motar ce lokacin da ta faɗa kogin da ke yankin Iyana-Oworo ɗauke da wasu mutane da ke halartar biki a yankin.

An ga yadda kayayyakin mutane suke iyo a saman ruwa tare da sauran abubuwan da ke cikin motar, Sai dai rahotanni sun ce mutanen da ke wucewa sun ceto dukkan fasinjojin.

Daga baya ne kuma wasu daga cikin fasinjojin suka ankara cewa ba su ga mutum ɗaya ba.

Daga bisani an ga wata mace kwance ba a cikin hayyacinta ba kuma nan take aka kai ta asibiti, inda ta rasu a can.

Hukumomi a jihar ba su yi ƙarin bayani ba ya zuwa lokacin kawo muku wannan labarin.