Home Labaru Sunan Eto’o Ya Fito A Jerin Mutanen Da Gwamnatin Spain Ke Tuhuma

Sunan Eto’o Ya Fito A Jerin Mutanen Da Gwamnatin Spain Ke Tuhuma

66
0

Hukumomin Spain sun ce, gwarzon tsohon dan wasan kwallon kafar Kamaru Samuel Eto’o ya ci bashin kusan Euro miliyan 1 na kudaden harajin da ya ki biya a lokacin zamansa a kasar.

Eto’o mai shekara 40 wanda kuma aka zabe shi a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamaru a kwanan nan, sunan sa ya bayyana cikin jerin sunayen mutanen da hukumomin Spain suka ce ana bin su bashin kudin harajin.

Eto’o wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na shekara har sau hudu, ya buga wa kungiyoyi da dama kwallon kafa a Spain da suka hada da Real Madrid da Barcelona kafin ya rataye takalmansa a 2019.

Ko a shekarar 2016, sai da masu shigar da kara na gwamnatin Spain suka zargi Eto’o da hada baki da wasu wajen kauce wa biyan harajin Euro miliyan 3.9 lokacin da yake taka leda a Barcelona.