Home Labaru Mohamed Salah Ya Ce Yana Son Karkare Sana’Ar Sa Ta Tamaula A...

Mohamed Salah Ya Ce Yana Son Karkare Sana’Ar Sa Ta Tamaula A Liverpool

14
0

Dan wasan tawagar Masar, mai shekara 29 Muhammad Salah ya ci kwallo 137 har da 12 da ya ci a kakar bana a wasa 214 da ya yi wa Liverpool, tun bayan da ta dauko shi daga Roma kan kan fam miliyan 34 a 2017.

Kawo yanzun dai kwantiragin Salah zai kare a karshen kakar badi a Liverpool amma ya ce idan aka tambaye shi zai so ya ci gaba da taka leda a Liverpool har lokacin da zai yi ritaya a kwallon kafa baki daya.

Salah ya kara da cewa kawo yanzu baya jin zai iya buga wasan da zai fuskanci Liverpool a wata kungiya domin abu ne mai wahala, kuma baya son jin wannan maganar, domin batun kan bata masa rai.

Salah ya fara taka leda ne a Al Mokawloon da ke garin su daga nan ya koma Basel sai kuma Chelsea daga nan ya je Fiorentina sai Roma, sannan Liverpool ta dauke shi.

Liverpool dai za ta ziyarci Manchester United a gasar Premier League ranar Lahadi, inda ake sa ran Salah zai ci kwallo a wasa na 10 a jere.